Yayin da hukumar zaben kasar Nijar ke tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar Dokokin da aka gudanar jiya Lahadi, masu sa ido na kungiyar tarayyar Afirka sun yabawa halin dattakon da ‘yan kasar ta Nijar suka nuna inda komai ya kammala ba tare da wani hargitsi ba.
WASHINGTON, DC —
Hajiya Aisha Abdullahi wata ‘yar Najeriya dake wakiltar kungiyar Tarayyar Afirka a wannan zabe na jamhuriyar Nijar ta gayawa wakilin Muryar Amurka, Sule Mumuni Barma, abubuwan da ta lura da su a zagayen da tayi a birnin Yamai.
Inda tace an bude guraren zabe akan idanunsu bayan shafe kwanaki a Jamhuriyar Nijar, sun kuma tattauna da Shugaban kasa da ma’aikatan da ke kula zabe da ma sauran al’ummar kasar. Ta kuma bayyana yadda mutanen Nijar ke da nutsuwa.
Baya ga matsalar isar kayan aiki da aka samu a wasu guraren zabe, babu wata matsala da zaben ya fuskanta, komai ya tafi yadda ake so.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5