Kwamitin shari’ar majalissar dattawa Amurka sun shirya jefa kuri’a akan wanda zai cike gurbin alkalen kotin kolin Amurka Brett Kavanough a yau juma’a, bayan jiya Alhamis an yini ana sauraran laifin da ake zargin shi, da Christine Blasey Ford ta gabatar akan laifin keta haddin ta.
Yan jam’iayar republican su goma 11 da yan democrats su 10, sune zasu yanke hukuncin ko su bada shawarar dukkan wakilan Majalisar su amince ko kuma a’a, inda ake sa ran fara shirin jefa kuri;ar a ranar asabar.
Amma Kungiyar lauyoyin Amurka jiya Alhamis da yamma ta bukaci yan majalissun su jinkirta zaben har sai hukumar bincike manyan laifu ta Amurka wato FBI, ta kara wani sabon bincike akan zargin da Ford da sauran matan sukai mashi.