Wakilan kasar Libya na neman bin hanyar diplomasiya wajen warware rudamin kasar

Babban gidan yarin dakarun Muammar Gaddafi da aka kona a Benghazi

Jami’an kasar Libya sun fara daukar matakan diplomasiya a yunkurin warware rudamin kasar, yayinda dakarun hadin guiwa na kasa da kasa suke ci gaba da luguden wuta kan mayakan gwamnati .

Jami’an kasar Libya sun fara daukar matakan diplomasiya a yunkurin warware rudamin kasar, yayinda dakarun hadin guiwa na kasa da kasa suke ci gaba da luguden wuta kan mayakan gwamnati kusa da inda ‘yan tawaye suke iko. Wata tawaga dake wakiltar shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi ta ce a shirye gwamnati take ta aiwatar da shawarar da KTA ta bayar. Tawagar ta bayyana haka ne jiya jumma’a bayan ganawa da kasashen nahiyar Afrika biyar a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha. Tawagar ta bayyana niyarta ta daina bude wuta ta kuma bukaci a daina kaiwa kasar hari ta sararin sama a kuma janye shinge da mayakan ruwa suka yiwa kasar. An gudanar da taron ne da ya kunshi tawagar kasar Libya bayan kiran da taron manyan kasashen duniya a Addis Ababa ya yi, na samar da tsarin damokaradiya da zai bada damar gudanar da zabe a kasar Libya. Tawagar kasar Libya ta je zauren taron, sai dai aka hana ta shiga, sabili da rashin halartar da wata kungiyar ‘yan tawaye ta Libya tayi. Gudanar da zabe a kasar Libya zai iya kawo karshen mulkin Mr. Gadhafi na tsawon shekaru 41. Jiya jumma’a har wa yau, kungiyar tsaro ta NATO tace Laftanar janar Charles Bouchard na kasar Canada shine zai jagoranci rundunar hadin guiwa a Libya. Ranar alhamis kungiyar hadin guiwar ta amince da karbar jagorancin aiwatar da hana shawagi ta sararin sama a Libya. Jiya dakarun hadin guiwar suka kai sababbin hare hare kan sansanan sojin kasar Libya dake kusa da garin Ajdabiya a gabashin kasar, wanda ke kimanin tazanar kilomita 160 kudu da Bengazi dake karkashin ikon ‘yan tawaye.