Wakar Hip-hop na regge' ya fara karbuwa a cikin alumma duba da yadda harkar ke fadakar da alumma baya ga nishadantar ba kamar yadda ake yi wa harkar kallon mai gurbata tarbiya ba inji wani matashin mawaki Umar Uba Ishaq wanda aka fi sani da Umar Khan.
Ya ce a can baya ana yi wa wakokin Hip hop kallon a wata hanya da ke gurbata tarbiya da ma dabi’un matasa alhali kuwa wakokin a lokuta da dama kan wa’azantar da jama’a akan zamata kewa da abubuwan cigaba.
Umar Khan ya ce ya fara wakar Hip hop ne bisa sha’awa domin a cewarsa baya ga wakar akwai harkar kasuwanci da yake yi a yanzu.
Ya kara da cewa a jamhuriyar Nijar, yake aiki daukar mafi yawan wakokinsa kasancewar Studio din da yake amfani dashi yana kasar ta Nijar. Yana kuma mai cewa kasancewar haka an fi sauraron wakokin nasa a kasar ta Nijar.
Your browser doesn’t support HTML5