Fim mai cike da wakokin nan da mawakiya Beyonce ta yi mai taken “Black is King,” wato Bakin Mutum Sarki Ne na cigaba da shan yabo da kuma suka a duniya, saboda yadda ya bayyana al’adar Afurka. A kasar Afurka Ta Kudu, inda aka hada wannan fim din mai tsawon minti 85, mutane da yawa sun ce wannan ha ma wuce fim.
Black is King, dai wani fim ne mai cike da wakoki wanda shahararriyar mawakiya kuma marubuciyar wakokin nan na Amurka, Beyonce ta jagoranci tsarawa, da harhadawa da kuma kammalawa.
Wannan fim din ya yi fice irin na wakarta mai taken “The Lion King: The Gift,” wato Sarakin Zagi: Baiwa. Bara ne aka yi fim din a Amurka, Kudanci da Yammacin Afurka, da kuma Turai, kuma ya kunshi mawakan Afurka da dama.
Wannan fim din, wanda aka fitar a watan Yuli, ya samu karbuwa matuka daga masu saurare, amma kuma akwai masu suka.
Wasu na cewa Beyonce, wadda aka haifa a birnin Houston na jahar Texas ta nan Amurka, ta ari abubuwan Afurka ba bisa ka’ida ba, musamman siffofin da su ka jibinci Afurka a fim din, alhalin kuwa a al’adance ba ta da wani tushe a nahiyar ta Afurka.
To amma a Afurka ta Kudu, sai ma murna wadanda su ka taka rawa wajen yin wannan fim din ke ta yi.
Sibusiso Mathebula, wani dalibi mai karanta harkar fim, ya ce an martaba shi da aka sa shi cikin masu yin fim din. Ya ce fim din ya burge shi. Fim din ya tabo abubuwa da dama wadanda ba a koya masu ba a makaranta game da tarihin bakar fata.
Ya ce lokacin da ya ga fim din ne ma ya fara ganin labarin da kuma tufafin da ta ke sawa da kuma daukacin abubuwan fim din, wanda hakan ya bullo da abubuwa da dama fiye ma da yadda aka zata zai faru.
Kgosi Motosoane mai son wakokin Beyonce y ace ‘yan Afurka da ke kasashen waje – ciki har da bakaken fatan Amurka – na da damar amfani da abin da was uke ganin kayan al’adun Afurka ne. Y ace shi dai y ana sha’awar fim din.
Kgosi ya ce an fai mayar da mata bakake can mataki na kasa a cikin al’umma. Don haka bullowarsu cikin al’amura masu matukar tasiri haka, abu ne mai karfafa gwiwa.
Dalibi mai karanta yadda ake fina-finai, Mathebula y ace fim din Beyonce ya sa shi sha’awar fara yin nashi fim din don ya dada yada bayanai game da Afurka.
‘Yan Afurka magoya bayan Beyonce sun yi muwafaka kan abu guda: Idan Bakin Mutum Sarki Ne, to Beyonce sarauniya ce.
Anita Powell ta nan Muryar Amurka ce ta hada mana wannan rahoton.