Waka Ita Ma Sana’a Ce Mai Zaman Kan Ta - Umar Ahmad Aliyu

A shirin mu na nishadi Dandalin VOA ya samu bakunci mawaki Umar Ahmad Aliyu, wanda aka fi sani da Baffa Amy mawakin na Hausa hip-hop, wanda yake cewa har kawo yanzu al’ummar gari na yi wa mawaka kallon mutane ne marasa da’a da suka rasa aikin yi.

Ya fara koyon waka ne da salon na kafiya, wanda a lokacin koyon yadda ake jira kafiya wakoki, Baffa Amy ya ce har sai da ta kai shi ga cike littafi biyu da kalaman kafiya, shekaru takwas da suka wuce, kuma kamar kowa sha’awa ce ta ja shi ga harkar waka.

Baffa Amy dai har kawo yanzu dalibi ne bai kamala karatunsa na Jami’a ba, ya ce yana hada waka da karatunsa a lokaci daya, sannan wakokin sa na mai da hankali ne wajen inganta yarensa da al’adunsa ta hanyar wakokinsa.

Baffa Amy ya ce yana isar da sakonnin cewar waka ita ma sana’a ce mai zaman kan ta, sabanin yadda mutane ke yi wa mawaka kallon sun rasa sana’ar yi.

Har ila yau akwai sakonnin da suka danganci shaye –shayen kwayoyi da matasa ke yi a yanzu, sai wakokin fadakarwa, daga cikin wakokin sa ya ce akwai wata wakarsa wacce yayiwa lakabi da "Arresting" wanda ke nuni da illa shan kwaya da ma mu’amala da masu shaye –shayen kwayar ga matasa da ba sa sha.

Babban burin Baffa Amy shi ne ya isar da sokannin fadakarwa sannan mutane su ilmatu tare da fahimtar abinda wakarsa ta kunsa cikin sauki da fahimta.

Your browser doesn’t support HTML5

Waka Ita Ma Sana’a Ce Mai Zaman Kan Ta - Umar Ahmad Aliyu 06'09"