Barrister Solomon Dalung wanda ya jagoranci tawagar kiristoci domin shan ruwa a gidan Shaikh Dahiru Usman Bauchi tare da al'ummar musulmi yace tunda dama can akwai kyakyawar alaka tsakanin musumi da kirista ya zama wajibi a kula da dangantakar.
Da yake jawabi ministan Solomon Dalung ya godewa Shaikh Dahiru Bauchi da yadda ya karbi tawagar da karamci da nuna kauna. Yace baicin abincin da suka ci tare ya basu shawarwari masu kyau da zasu kawo zaman lafiya tsakanin musulmi da kirista. Kana ministan ya roki matasa su sa kunne kan koyaswar da zata zaman masu da anfani amma su gujewa duk wata koyaswar akida ta rikici da fitina domin bata da tushe a cikin littafan addinan biyu. Yace su "alulkitabi" suna da dangantakai mai kyau da musulmi. Yace zasu cigaba da dangantakar da yin muamala da cigaba da goyon bayan juna domin a gina kasa mai zaman lafiya.
Da yake mayarda marani Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya jaddada alakar dake tsakanin musulmi da kirista tun fil azar. Yace ya yi murna Solomon Dalung bai manta 'yanuwansa da ba minista ba har ya iya zuwa gidansa.Yace jama'arsa sun ji dadi da zuwansu. Yayi murna da fastocin da ministan ya zo dasu.Yace sun tuna masu dangantaka dadaddiya dake tsakanin musulmi da kirista tun lokacin Annabi Muhammad (SAW). Yace wannan zai farkar da mutane su gane tsakanin musulmi da kirista babu gaba.
Su ma fastocin dake cikin tawagar minisran sun bayyana jin dadinsu suna cewa abun da ya faru babban daratsi ne ga kowa.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5