Gwamnan yana neman a kafa wata doka ta musamman da zata baiwa shugaban kasa da majalisaar zartaswa ta kasa ikon gudanar da harkokin tattalin arziki ba tare da kawo wani tarnaki ba.
Gwamnan yace samun dokar zata taimakawa gwamnati wajen ganin ta fitar da kasar daga halin da take ciki a yanzu na tabarbarewar tattalin arziki. Yace farfado da tattalin arzikin na bukatar a aiwatar dashi cikin gaggawa.
Masana da masu sharhi akan tattalin arziki sun yi tsokaci akan furucin na babban bankin. Dr. Dauda Muhammad masanin tattalin arziki na jami'ar Bayero dake Kano yace idan kasa ta fada cikin tabarbarewar tattalin arziki akwai matakan gaggawa da na tsakiya da kuma na dogon lokaci da ya kamata a dauka domin farfado da tattalin arzikin.
Cikin mataki na dogon lokaci shi ne ganin kasa ta fita daga dogaro ga hanya daya tilo ta samun kudin shiga kamar yadda lamarin yake a Najeriya yanzu. Ya kamata a kaucewa maganar dogaro ga man fetur. Mataki na tsakiya shi ne kasa ta kara kudin da take kashewa a cikin gida. Mataki na gaggawa shi ne tallafi da za'a iya ba masu karamin karfi, walau na kudi ko na abinci saboda rage masu radadin tsadar rayuwa.
Dr Dauda Muhammad yace a Najeriya akwai wasu dokoki da suke da wuya a yi aiki dasu cikin gaggawa da zasu kawo cikas wurin farfado da tattalin arziki idan ba'a kawar dasu ba. Misali, dokar sayen kaya sai an kawar da ita zata sayi kaya a gurguje ba tare da bata lokaci ba.
Masu sharhi akan tattalin arziki sun ce dole ne fa gwamnati ta fadada hanyoyin samun kudaden waje domin rage tsadarsu. Alhaji Kasumu Garba Kurfi wani masanin tattalin arziki kuma mai hada-hada a kasuwar saka hannun jari yace duk kasar da bata sarafa wasu abubuwa ta sayar a waje ba zata iya kawowa kudin kasarta daraja ba.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5