Rahotanni daga mujallar Record sun bayyana cewa Barcelona zata bayar da Philippe Coutinho ko kuma Ousmane Dembele ga kungiyar kwallon kafa ta Paris-Saint German, domin ganin sun dawo da tsohon dan wasansu Neymar.
Real Madrid ta bayyana cewa ta ware fam miliyan £115, da zata ba Chelsea a matsayin kudin da za su biya dan sayan Eden Hazard, kamar yadda jaridu suka ruwaito.
Tsohon kocin Chelsea Antonio Conte, ya sanya hannu a yarjejeniyar kwantirakin shekara uku, don zama kocin kungiyar kwallon kafa ta Inter Millan har zuwa 2022, shekara biyar kenan rabon da Conte ya horar da wata kungiya a kasar Itali.
Shi kuwa dan wasan gaba na Manchester United Romelu Lukaku, ya amince da rage albashinsa a kungiyar domin ya samu damar komawa kulob din Inter Milan a kaka mai zuwa,
A nasa bangaren kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer, ya sanya wa'adin zuwa karshen shekarar badi domin sayar da dukkanin wani 'yan wasan da ba za a ci gaba da tafiya da su ba a kulob din.