Wai Yara 'Yan Matan Chibok na Raye Kuwa?

'Yan matan Chibok

A kokari da wannan gidan radiyon yake wajen ganin a dawo da wannan yara da wasu ‘yan ta’adda suka sace kimanin kwanaki dari uku da sittin da biyar kennan. Wasu iyaye sun bayyana damuwar da suke ciki, duk da cewar ba ‘yayansu bane amma dai dole ne iyaye su kansance cikin damuwa idan haka ta kasance da nashi.

Malama Matha, tayi karin haske ganin yadda take tunanin iyayen wadannan yara suke ciki, don tana ganin wadannan iyayen yara suna cikin wani tashin hankali saboda suna tunani wai wane irin hali ‘yayansu ke ciki gani an kwashe wadannan kwanakin masu dama babu wani bayani inda wadannan yaran suke, don zasu fi samun kwanciyar hankali idan aka ce wadannan yaran sun mutu da ace suna hannun wasu ‘yan ta’adda kuma ba’a san wane irin hali suke ciki ba.

Itama dai Malama Amina Hanga, shugaban gidauniyar Isah Wali, batayi shuruba inda take bayyana nata irin halin da tasamu kanta cikin tun bayan sace wadannan yaran, dama wasu mata iyaye yadda zasu dauki wannan abun al’ajabin.

Ta nuna wannan a matsayin wani babban abun damuwa da shiga cikin halin damuwa da iyayen wadannan yaran suka samu kansu, don haka suna kara kira da gwamnati tayima Allah ta yi amfani da karfin soji da take da su da su shiga cikin wannan sunkurun dajin na Sambisa don ceto wadannan yara ko Allah yasa iyayensu su samu kwanciyar hankali.

A bangare daya kuma, suna mika kukansu ga Allah kuma suna rokon wannan sabuwa gwamnatin me zuwa da tayi kokarin sa wannan matsalar a matsayin abu na farko da zasu fuskanta idan Allah yasa sun shiga ofis nan da wasu kwanaki masu zuwa. Don suna gani wannan wani abu ne da yakamata ace gwamnati ta bama fifiko, tayi yunkuri don kwantar da hankalin al’umar kasarta, a kowane hali.

Babban rokon al’uma shine asamamusu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa, wanda yake hakki ne daya rataya akan gwamnati.