Yanzu shekaru hudu kenan da Kanar Sambo Dasuki, tsohon mai ba wa Shugaban Najeriya Shawara ta fuskar tsaro a zamanin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, yake a tsare.
Sambo, wanda hukumar EFCC ke tuhuma da salwantar da kudin da su ka haura dala biliyan 2, na hannun jami’an tsaron farin kaya, DSS.
Bayan an kama Dasuki, mahaifinsa tsohon Sarkin Musulmi, sultan Ibrahim Dasuki, ya yi jinya har Allah ya yi masa rasuwa ba tare da Sambo ya samu ganawa da shi ba.
Kazalika, Sambo Dasuki ya samu beli har ma daga kotun kungiyar kasashen raya tattalin arzikin Afurka ta yamma ECOWAS/CEDEAO amma bai samu fitowa ba.
Ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana dalilan rashin sake Dasuki, ciki har da batun kudin da a ka ce an ware ne don sayo makamai amma ba a sayo ba, har hakan ya yi sanadin kashe dubban mutane da 'yan ta'adda su ka yi.
A hirarsu da Muryar Amurka dai kusan lokaci zaben 2015, Dasuki ya bayyana cewa shi ne kan gaba wajen neman kawo maslaha a gwagwarmayar kawar da Boko Haram.
Da alamun Sambo Dasuki na nan lafiya a hannun hukuma kuma ba a san ranar da shari’ar sa za ta kammala, har ya kai ga yanke ma sa hukunci ba.
Shi ma shugaban ‘yan shi'a na IMN Ibrahim El-zakzaky zai cika shekaru 4 a watan nan na Disamba tun kama shi da a ka yi a Zaria biyo bayan arangamar ‘yan shi'a da sojoji da aka fara a cibiyar Hussainiyya.