Wadanda Suke Jira Najeriya Ta Wargaje Za Su Ji Kunya – Osinbajo

Mataimakin Shugaban Najeriya Prof. Yemi Osinbajo (Instagram/ Prof. Osinbajo).

Taron matasan na APC na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriyar ta tsinci kanta a cikin wani yanayi na kiraye-kirayen da kungiyar IPOB ke yi na a raba kasar.

Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi kira ga matasa da su yi iya bakin kokarinsu wajen ganin kasar ta ci gaba da zama a dunkule.

Osinbajo ya yi kiran ne yayin wani jawabi da ya yi a wajen babban taron matasan kasar na farko da aka yi Abuja wanda matasan jam’iyyar APC suka shirya, kamar yadda wata sanarwa da hadimin Osinbajo kan yada labarai Laolu Akande ya fitar.

A cewar Osinbajo, “wadanda suka ja gefe suna jira Najeriya ta wargaje, za su sha kunya, saboda ina da tabbacin cewa ku da kuke zaune a nan a yau, za ku hana hakan aukuwa."

Mataimakin shugaban Najeriyar, wanda shi ne babban bako a taron da aka yi masa taken “Makomar Ita Ce Daukan Matsaya,” ya kara da cewa, idan matasa suka shiga cikin siyasa don a dama da su, hakan zai taimaka wajen samar da sauyi mai ma’ana.

Zauren taron da matasan APC suka shirya a Abuja (Facebook/Bashir Ahmad)

Karin bayani akan: APC, Yemi Osinbajo, IPOB, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Osinbajo, wanda ya nuna bai gamsu da adadin matasan da ake damawa da su a fagen siyasar Najeriyar ba, ya kara da cewa akwai bukatar wadanda suka riga suka shiga, su iya bakin kokarinsu, su janyo hankali sauran matasan don a dama da su.

“Daga iya adadin matasan da suka fita zabe kadai, ya isa mutum ya gane cewa dumbin matasa ba su yi rijista ba, ko ba su fita yin zabe ba.”

“Akwai hakki da ya rataya a wuyanku, na ku kwadaitar ku kuma ja hankalin sauran matasa” don shiga fagen siyasar.

“Muhimman batutuwa, samar da maslaha, da bullo da dabaru duk daga wurinku za su fito, domin wannan lokaci naku ne.”

Taron matasan na APC na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriyar ta tsinci kanta a cikin wani yanayi na kiraye-kirayen da kungiyar IPOB ke yi na a raba kasar da kuma yunkurin da ake yi na sauya kundin tsarin mulkin Najeriyar.

Ko da yake, a karshen makon da ya gabata, gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya da kungiyar ta IPOB take, sun nesanta kansu da yunkurin kungiyar na neman a raba kasar.