Wadanda Suka Tsira Daga Hatsarin Jirgin Saman Indiya Sun Ce Jirgin Ya Yi Ta Mummunar Girgiza
Your browser doesn’t support HTML5
Jirgin kwasar jama’a na musamman da ke kai mutane gida Indiya, wadanda su ka makale a kasashen waje saboda matakan cutar coronavirus ya kauce hanyar gudun tashi, ya rabe gida biyu jiya Jumma’a a Kerala, ya kashe mutane akalla 16, ya kuma raunata wasu 123 a cewar ‘yan sanda.