Wadanda Suka Kamu Da Cutar Korona A Rana Daya A Najeriya Sun Haura Dubu 1

Allurar rigakafin Covid 19

Gwamnatin Najeriya ta ba da rahoton cewa sabbin mutane sama da dubu 1 ne suka kamu da cutar korona birus a rana ta biyu a jere.

Hakan na kunshe ne a cikin bayanai daga cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya wato NCDC.

Da take bayar da karin haske kan bullar cutar a kasar, hukumar, a wani sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma'a, ta bayyana cewa an samu sabbin mutane dubu 1 da 51 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar.

Duk da haka dai adadin rahoton wadanda suka kamu da cutar a ranar alhamis ya yi kasa da dubu 1 da 424 da aka ruwaito a ranar talata.

Adadin na ranar laraba shi ne mafi girma da aka samu a cikin watanni shida da suka gabata ko da yake ba a sami rahoton mutuwa ko daya ba a ranar Alhamis.

An sami adadin sabbin mutane dubu 1 da 51 da suka kamu da cutar a cikin jihohi 10 hade da babban birnin tarayya Abuja.

Jihohin dai sun hada da Legas mai adadi 599, babban birnin tarayya Abuja da adadi 238, Ribas 79, Oyo 51, Ondo 32, Filato 20, Akwa Ibom 11, Ogun bakwai, Bayelsa biyar, Kano biyar, da kuma jihar Kwara mai hudu.

A cewar hukumar NCDC, ba a samu wani sabon mutum da ya kamu da cutar ba a jihohin Bauchi, Ekiti, Osun, da kuma Sokoto.

A sakamakon haka, adadin wadanda aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar ta COVID-19 a jimlace tun farkon bullar cutar a Najeriya ya karu zuwa dubu 221 da 71.

Tun bayan bullar cutar a kasar a karshen watan Fabrairun shekarar 2020, an sallami jimillar mutane dubu 211 da 345 da suka kamu da cutar sannan an samu mutuwar mutane dubu 2 da 983.

Hukumar NCDC ta tattara tare da yin gwaji a kan samfurin mutane miliyan 3 da dubu 686 da 403, a yayin da akwai mutane dubu 6 da 743 har yanzu da ke dauke da cutar a jimilance a jihohi daban-daban ciki har da babban birnin tarayya Abuja.