Duk da bayanan da su ka biyo bayan sace mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar lahadi da la'asar, da ke cewa an ceto mutum 9 amma biyu da su ka hada da direban motar safa sun rasa rayukansu.
Daliban, su 15 dai sun taso ne daga Kaduna a kan hanyarsu ta tafiya cibiyar harshen Faransanci da ke Badagary a jihar Lagos lokacin da akasin ya rutsa da su.
'Yar uwar daliban da ke aji na uku a jami'a, ta ce masu satar sun buga waya su na bukatar kudin fansa Naira miliyan 30 kan kowane dalibi da jimillar kudin ta tashi Naira miliyan 450.
Maimakon bukatar a yi amfani da karfi wajen ceto daliban, matar da ta bukaci a boye sunan ta don nasarar cinikin kudin diyyar, ta nemi a roki masu satar su rage kudin ko kuma su tausayawa daliban da ya ke talakawa ne.
Wakilin sashan Hausa, Nasiru Adamu El-Hikaya na daga cikin wadanda Allah ya kubutar daga masu satar, domin ankara da su ka yi daf da inda barayin su ke a yankin Katari, hakan yasa soka koma baya. Sai dai Nasiru ya ce basu ga jami'an 'yan sanda a kan hanyar ba, sun kuma jira har sai da lamarin ya lafa, sannan suka yi kwambar motoci suka kuma iske motocin wadanda lamarin ya rutsa da su.
Alhaji Muhammadu Murtala dattijo mazaunin Kaduna, da kan bi hanyar ya ce da safe ba a samun cin karo da masu satar in an kwatanta da yadda lamarin ke ke faruwa da yamma.
In za a tuna a watannin baya babban sufeton 'yan sanda Muhammadu Adamu, ya ce ba wani hatsari ga bin hanyar, yanzu kuma sai gashi wannan lamari ya faru.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5