Wadanda ake sa ran zasu fafata wajen maye gurbin Biden akwai ita kanta Kamala Harris, mataimakiyar sa yanzu sun hada da Kamala Harris, mai sekaru 59, al’umma da yawa suna ganin mafi dacewa shine ta maye gurbin Biden, saboda Kwarewarta ta na yin aiki a matsayin mataimakiyar shugaban kasa tare da Biden.
Sai kuma Gretchen Whitmer, mai shekaru 52, wadda ta ke cikin wa'adinta na biyu a matsayin gwamnan jihar Michigan.
Whitmer Ita ce mataimakiyar shugabar Kwamitin Kasa na jam’iyyar Democrat, kuma ta samu nasarar lashe yakin neman zabenta na gwamna cikin sauki a jihar, inda ta lashe zabe da sama da maki kashi 9 cikin 100 a zabukan da ta yi takara a 2018 da 2022.
Na ukun su kuma shine Gavin Neswom mai shekaru 56, wanda ya dade a harkokin siyasar California, kuma a halin yanzu shine gwamna. An zabe shi a shekarar 2019 kuma ya lashe zaben da sama da kashi 20 cikin 100.
Newsom kwanan nan ya rattaba hannu kan wata doka a California ta zama jiha ta farko da ta haramtawa malaman makaranta sanar da iyayen yara idan daliban suna son canza jinsin su.
Akwai kuma Pete Buttigieg, mai shekaru 42, wanda aka nada shi a matsayin sakataren sufuri a shekarar 2021. Ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2020 kuma ya yi rawar gani sosai a jam'iyyar, inda ya kusa lashe zaben fidda gwani a New Hampshire.
Butigieg dan South Bend ne, dake jihar Indiana, inda aka zabe shi a matsayin magajin garin a 2012 kuma ya yi aiki har zuwa 2020.
Idan aka zabe shi, Buttigieg zai zama shugaban kasa na farko dan Luwadi a Amurka.
Akwai kuma Gwamnan Jihar Pennsylvania Josh Shapiro, mai shekaru 51, kuma ya taka muhimmiyar rawa a jihar da ta zabi Trump a shekarar 2016, inda inda aka zabi Biden a shekarar 2020.
Ana ganin Shapiro a matsayin wanda zai iya zama mataimakin shugaban kasa idan Harris ta maye gurbin Biden akan tikitin, saboda zai iya kawo sakamakon zabe mai karfi musamman a Al’ummar dake da bambance-bambancen.
Na karshen su kuma shine Andy Beshear, mai shekaru 46, ya samu karbuwa a tsakanin 'yan jam'iyyar Democrat saboda nasarar sa a jihar Kentucky, mai rinjayen ‘yan jam'iyyar Republican. Beshear yana cikin wa'adinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar Kentucky bayan ya doke tsohon lauyan gwamnati Daniel Cameron da kashi 5 cikin 100 a shekarar 2023.
Kamar Shapiro, ana ganin Beshear a matsayin wanda zai iya zama mataimakin shugaban kasa idan Harris ta zama ‘yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar Democrat.
Shugaban kwamitin jam'iyyar Democrat, Jaime Harrison, ya fada a cikin wata sanarwa cewa jam'iyyar "za ta bi tsari na gaskiya da adalci" don zaben "dan takarar da zai iya kayar da Donald Trump a watan Nuwamba."
Ku Duba Wannan Ma Abinda Shugabannin Kasashen Duniya Ke Cewa Game Da Janyewar Biden Daga Takarar Shugaban Kasa