Kamar yadda muka saba jin ra’ayoyin matasa akan al’amurran rayuwa musamman ta bangaren soyayya, wannan makon mun nemi jin ra’ayoyin su ne akan irin kyautar da tafi dacewa samari sub a ‘yan mata a sakamakon irin albarkacin bakin da jama’a ke tofawa akan amfani da kudi wajan yaudara.
Jama’a da dama a wurare daban daban sun bayyana ra’ayoyin su akan yadda ake amfani da kudi wajan yaudarar wasu ‘yan mata, dan haka idan matashi yana so ya kauce ma wannan zargi wacce irin kyauta ya kamata ya rika ba masoyiyar sa?.
Da farko dai kusan kashi sava’in da biyar cikin dari na samarin sun nuna cewar basu ba ‘yan matan su kudi, kuma a cikin jerin kyaututtukan da suka zaiyana kusan dukkan su sun nuna cewar kasancewar mata ‘yan kwalliya ne, sukan mutunta kayan kwalliya irin su turare da man shafawa da makamantan su a matsayin kyauta.
Daga karshe wasu daga ciki sun kara da cewar idan budurwa ta saba da amsar kudin saurayi takan zamo mai wuyar al’amari domin kuwa muddin aka dauki lokaci mai tsawo ba tare da ya bata kudi ba to akan sami matsala.
Ga cikakkiyar hirar.