Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudi Basa Siyan Soyayya Amma Soyyaya Na Siyan Komai A Rayuwa


Mai kudi yan China
Mai kudi yan China

Soyayya kan hada ko raba mutun da abubuwa da dama a rayuwa. Mr. Yao Nanshan, mai shekaru sittin da haihuwa, dan asalin kasar China ne. Ya zama hamshakin mai kudi a sanar da ya fara shekaru talatin da suka wuce na gidan abinci a kasar Spain.

Bayan kwashe shekaru da dama yana zaune a cikin babban birni, yana gudanar da rayuwar shi kamar kowa. Cikin rana tsaka sai ya haddu da wata mace da yake matukar so, mai suna Liu Lijuan, ita kuma tana zaune a wani kauye. Sunyi aure bayan tarayyar sun a wasu lokkutta. A shekarar 2002 matar shi ta mutu, wanda hakan ya sashi cikin wani hali na rayuwa.

A shekarar 2013, hamshakin mai kudin da abokin shi sunyi tafiya zuwa wani tsibiri, inda suka kuskure motar su ta komawa gida. Hakan yasa sun shiga cikin wani hali, domin kuwa mota kanje tsibirin ne sau daya a rana. Abu daya da ya rage musu shine su kwankwasa gidan mutane, su nemi makwanci har zuwa da safe. Koda suka kwankwasa gida na farko sai su kayi dace da gidan Liu ne, ta karbe su hannu biyu, wanda daga nan soyayyar su ta fara. Ta gaya mishi cewar idan yana son zama da ita, sai dai ya bar dukiyar shi a birni ya dawo kauye su fara wata rayuwa, wanda kuwa hakan akayi. Ya koma kauye ya bar dukiyar shi a birni.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG