An tarbi Putin ne a wasu jerin gwanon motoci zuwa masaukinsa dake birnin Nagoto, inda nan ne garin iyayen Abe, jim kadan bayan da jirgin sa ya sauka da yammacin yau Alhamis. A jiya Laraba ne Fara Minista Abe ya fada wa manema labarai a birnin Tokyo cewa, yana fatan zasu zauna domin cimma da yarjejeniya da Putin.
Ana sa ran shugabannin biyu dai zasu kammala tattaunawar ne gobe Juma’a a babban birnin kasar Japan.
A baya dai shugaba Abe yayi fatan samun matsaya kan takaddamar da ake kan tsibirai hudu dake bakin tekun Arewacin Japan, da aka fi sani da yankunan Arewaci a Japan, da kuma Yammacin tsibirin Kurils a Rasha. Sojojin Tarayya Soviet ne suka kwace tsibirin a shekara ta Alif 945, suka tilasta wa ‘yan kasar Japan Dubu 17 ficewa daga tsibirin. Marigayi mahaifin Fara Minista na yanzu yayi kokarin sasantawa da Rasha shekaru 30 da suka gabata amma hakka ba ta cimma ruwa ba.