Kakakin kungiyar yan tawayen ta Nour el-Din el-Zink, Yasser al-Youssef shine ya bayyana yarjejeniyar a jiya Talata da kasashen Rahsa da Turkiya suka shiga Tsakani wadda zata fara aiki nan da wasu sa’o’i.
Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya ko MDD Vitaly Churkin ya tabbatarwa manema labarai da wannan yarjejeniyar tun kafin zaman gaggawa na kwamitin sulhun MDD a kan birnin Aleppo wanda Faransa da Birtaniya suka kira.
Jakadan yace sun samu labarin tsagaita ayyukan soji a gabashin birnin Aleppo, kuma yankin ya sake komawa karkashin rikon gwamnati, don haka za'a iya gudanar da manyan ayyukan agaji a yankin.
Churkin yace akasarin mayakan suna barin gabashin birnin Aleppo suna komawa garin Idlib.
Sai dai kuma manzon MDD a Syria Staffan de Mistura ya bayyana damuwarsa cewar garin Idlib zai iya zama wurinda munanan hare haren zasu koma.