Uwargidar Shugaban Amurka Ta Ziyarci Nelson Mandela A Afirka Ta Kudu

Uwardidar Shugaban Amurka, Michelle Obama da tsohon Shugaban Afirka ta kudu Nelson Mandela

Uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama, ta kai ziyarar da ba a sanar za ta kai ba tun da farko, ga tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela, a farkon fara ziyarce-ziyarce a kasar.

Uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama, ta kai ziyarar da ba a sanar za ta kai ba tun da farko, ga tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela, a farkon fara ziyarce-ziyarce a kasar.

Mrs Obama ta gana da shi wannan barden yaki da bambancin launin fata dan shekaru 92 din a gidansa da ke birnin Johannesburg. ‘Yayan Mrs Obama su biyu wato da Malia da Sasha da kuma mahaifiyarta Marian Robinson, sun mata rakiya.

Wani hoton da Gidauniyar Nelson Mandela ta rabar na nuna Mr. Mandela zaune ganga da Mrs Obama kan wata kujera.

Tun bayan da aka yi wa Mr. Mandela jinyar matsalar numfashi a watan Janairu ne dai aka shawarce shi ya rinka yi komai a gida. Bai cika amsar baki ba.

Uwargidar Obaman ta na kan ziyarar Afirka ne na tsawon sati guda, lokacin da za ta karfafa batun tayar da komadar matasa, da karfafa gwiwa wa matasan Afirka su yi gaba-gaba wajen kokarin warware matsalolin nahiyar das u ka hada da talauci, da cututtuka da kuma canjin yanayi.

http://www.youtube.com/embed/272JCYBTaLU