Uwargida Michelle Obama Tana Cika Shekara Guda Da Shirin Yaki Da Kiba A Tsakanin yara

Uwargida Michelle Obama, matar shugaban Amurka.

Mai dakin shugaban Amurka tana rangadin kwanaki biyu a New York domin tallata wannan shiri na kare lafiyar yara daga kiba mai tsanani

Uwargidan shugaban Michelle Obama tana bukukuwan cikar shekara guda da kaddamar da wani shirinta mai suna "Let's Move" wanda aka tsara da nufin yakar yadda yara kanana ke yin kiba fiye da kima.

Jiya laraba, Mrs. Obama ta tafi New York domin rangadin wayar da kai na kwanaki biyu, inda aka shirya zata tattauna shirin a wasu shirye-shiryen telebijin guda biyu masu farin jini.

Uwargidan shugaban Amurka ta fada cikin wani shirin gidan telebijin na ABC (live With Regis and Kelly) cewa Amurka ta cimma tazara wajen yaki da kiba fiye da kima, amma har yanzu akwai sauran namijin aiki a gaba.

Har ila yau Mrs. Obama ta halarci wani shirin labarai da al'amuran yau da kullum na gidan telebijin na NBC mai suna "Today" inda ta ce shirin nata na inganta lafiyar yara, shiri ne na tabbatar da cewa yaran su na cin irin abincin da ya dace, kuma da yawan da ya dace, matakin da ta ce shi take aiki da shi a kan 'ya'yanta biyu, Sasha mai shekaru 9 da haihuwa da kuma Malia mai shekaru 12 da haihuwa.

A jiya laraba da maraice, uwargidan shugaban ta yi tattaki zuwa Jihar Georgia dake kudu maso gabashin Amurka domin ziyartar wata makarantar da ta rungumi wannan shiri nata na yaki da kiba fiye da kima. Har ila yau ta yi magana a cikin wani coci.

A cikin shekara guda da ta shige, Mrs. Obama ta samu goyon baya sosai ga wannan shiri nata, inda har majalisar dokoki ta zartas da wani kudurin dokar tabbatar da yara su na cin abincin da ya dace, shirin da zai lashe dala miliyan dubu 4 da dari biyar. A watan da ya shige kuma, jerin kantuna mafiya girma a duniya, Wal-Mart, ya yarda zai rage yawan sikari da gishiri da lkuma kitsea cikin dubban kayayyakin kwalama da yake sayarwa domin nuna goyon baya ga wannan shirin.