Asusun talafawa yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya , UNICEF na fadakar da 'yan jarida game da illolin aurad da yara mata da ba su kai shekaru 18 da haihuwa ba.
WASHINGTON DC —
Wakilin UNICEF ya bayyana cewa, tunkarar matsalar aurad da yara mata masu kananan shekaru tamkar gwagwarmaya ce da matsalolin da ke da nasaba da tattalin arziki, da al'adu, da yaki da talauci. A saboda haka 'yan jarida na da rawar da zasu taka a wannan fannin. Ganin yadda suke da karfin fada a ji a cikin al'umma.
Shugaban ma'aikatar da ke kula da inganta rayuwar mata,da bada tallafi ga yara kanana reshen Tahoua Mallam Alhassan Isa, ya kara jaddada muhimmancin wannan lamari idan aka yi la'akkari da yadda yake da nasaba da take hakkin yara kanana kuma auren wurin na aukuwa sosai a jihar Tahoua.
Saurari rohoton
Your browser doesn’t support HTML5