Umurnin Hana Fita A Kudu Maso Gabashin Najeriya Bai Yi Tasiri Ba

Akwai alamun cewa umurnin hana fita da kungiyar ‘yan awaren Biyafara ta IPOB ta ayyana a duk fadin yankin kudu maso gabashin Najeriya, bata yi tasiri ba yayin da harkoki ke ci gaba da tafiya kamar yadda suke a yawancin manyan biranen yankin. ciki har da Awka, babban birnin jihar Anambara.

Malama Mary-Jane Ibe wata mazauniyar Owerri, babban birnin jihar Imo ta ce, “na bi ta shaguna yanzun nan, kuma ‘yan kasuwa na ta bude shuganansu. Akalla, kashi 50 cikin 100 sun riga sun bude yanzu. Gaskiyar lamarin shine akwai cinkoson jama’a akan tituna.”

Dukes Chinedu, wani mazaunin birnin Inugu shima ya kara da cewa “Komai lami lafiya a Inugu, kowa na gudanar da harkokinsa yadda aka saba, ba a bi wannan umurnin ba saboda kowa ya fita yana gudanar da harkokinsa.

Shima wani magidanci, Mista Ikechukwu Uzom, ya ce, "hakkikanin gaskiya inaso in je gona in samarwa iyalina abinci’’. Matukar na zauna a gida bana tunanin zan samu abin ciyar da iyalina, saboda haka, dole ne in fita neman abin yi, in kuma ciyar da iyalina.” Yanzu haka dai jihar Abia 'yan asalin garin ne kadai suka bi umurnin hana fita.

Tun karshen watan Agusta ne kungiyar ta ayyana yau Juma’a, 14 ga wata, a matsayin ranar nuna fushi ga gwamnatin tarayyar Najeriya kan bacewar madugun nasu, Mista Nnamdi Kanu da iyayensa, tun ranar 14 ga watan Satumbar bara, shekara daya Kenan dai dai.

Your browser doesn’t support HTML5

Umurnin Hana Fita A Kudu Maso Gabashin Najeriya Bai Yi Tasiri Ba 3'39