Ukraine: Tsohuwar Jakadiyar Amurka Za Ta Bayyana A Gaban Majalisar Wakilai

Tsohuwar jakadiyar Amurka a Ukraine (zaune a tsakiya) Marie Yovanovitch, zaune a tsakiya

Tsohuwar jakadiyar Amurka a Ukraine, na shirin bayyana a gaban kwamitocin majalisar wakilan Amurka da ke jagorantar binciken da mai yiwuwa ya kai ga tsige shugaba Donald Trump, sai dai babu tabbas ko kwamitocin za su iya gudanar da zaman na yau Juma’a da Marie Yovanovitch.

Ita dai Fadar White House ta ki ba da hadin kai a binciken, wanda ta ayyana shi a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Baya ga haka, ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ita ma ta dakile wani yunkuri na gayyatar jakadan Amurka a Kungiyar Tarayyar Turai, Gordon Sonland daga gurfana a gaban kwamitocin domin ba da bahasi.

Ana dai zargin Trump ne da tirsasa Shugaban Ukraine ya yi bincike kan dan tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden, wato Hunter da nufin neman abin bata mai suna, zargin da Trump din ya sha musantawa.