Ukraine: Kamfanonin Air Peace, Air Max Za Su Fara Jigilar Kwaso ‘Yan Najeriya

'Yan Najeriya a Ukraine yayin da suke magan da masu aikin sa-kai

Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum dubu 520 ne suka fice daga Ukraine, wadanda mafi akasarinsu suka doshi Poland.

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta zabi kamfanonin jiragen sama na Air Peace da Air Max a matsayin wadanda za su yi jigilar kwaso ‘yan ‘yan Najeriya da suka tsallaka wasu kasashe da ke makwabtaka da Ukraine mai fama da rikici.

Ministan harkokin Najeriya, Geoffrey Onyeama ne ya bayyana hakan a wani taro da suka yi da Kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila a ranar Litinin.

Za a fara aikin jigilar kwaso ‘yan Najeriyar a ranar Laraba idan Shugaba Muhammadu Buhari ya amince, Onyeama ya kara da cewa.

Masu zanga-zanga a Abuja, suna kira da dakatar da yaki a Ukraine a kuma kwaso 'yan Najeriya da suka makale, Fabrairu. 28, 2022. (Timothy Obiezu/VOA)

Daruruwan ‘yan Najeriya da ke zaune a Ukraine, wadanda galibinsu dalibai ne sun tsallaka kasashen Poland, Romania da Hungary domin neman mafaka.

Kiyasin baya-bayan nan da ma’aikatar wajen harkokin Najeriya ta fitar ya nuna cewa mutum 150 sun isa Bucharest, babban Birnin Romania.

An kuma yi hasashen wasu mutum 200 za su isa Budapest, babban Birnin Hungary a ranar Litinin.

Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare NiDCOM , ita ma ta tabbatar da ambaci Air Peace a matsayin daya daga cikin kamfanonin da za su yi jigilar kwaso ‘yan Najeriyar.

Masu goyon bayan Ukraine suna zanga-zanga a birnin New York ranar 28 ga watan Fabrairu, 2022, a New York.

“Ofisoshin harkokin wajen Najeriya a Poland, Hugary da Ukraine, na aiki tukuru yayin da muke fara aikin kwashe (‘yan Najeriya) da kamfanin Air Peace kamar yadda aka saba.” Shugabar NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa ta wallafa a shafinta na Twitter.

Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum dubu 520 ne suka fice daga Ukraine, wadanda mafi akasarinsu suka doshi Poland.

Ana kuma fargabar cewa nan da wasu kwanaki ko makonni masu zuwa, adadin zai kai mutum miliyan hudu, shugaban hukumar Martin Griffiths ya ce.