Hukumar Kwallon Kafar Nahiyar Turai UEFA, ta kaddamar da bincike kan wata dabi’a mara kyau da ake zargin dan wasan Ingila Jude Bellingham ya nuna a lokacin da yake murnar zura kwallo a ragar Slovakia.
A ranar Lahadi Ingila ta kara da Slovakia a zagayen ‘yan 16 a gasar kwallon kafa ta nahiyar turai da ake yi a Jamus inda ta yi nasara da ci 2-1.
Slovakia na gaba da kwallo guda, ana kuma gab da tashi a wasan a lokacin da Bellingham ya ceto Ingila da wata kwallo mai ban sha’awa da ya doka, wacce ake wa lakabi da “bicycle kick” a turance a minti na 95.
Bayanai sun yi nuni da cewa Bellingham ya sa hannu ya kama gabansa a lokacin da yake murnar zura kwallon, wanda hakan dabi’a ce da aka haramta a wasan kwallon kafa.
Idan har aka samu Bellingham da laifi, akwai yiwuwar a haramta masa buga wasa na gaba a matsayin hukunci.
Dan wasan Ingila Harry Kane ya zura kwallo ta biyu wacce ta ba Ingila damar zuwa zagayen Quarter-final inda za su kara da Switzerland a ranar Asabar.