UEFA Na Binciken Barcelona Kan Zargin Biyan Alkalin Wasa

'Yan wasan Barcelona suna murnar cin kwallo

Wasu takardun kotu sun nuna cewa Barcelona ta biya dala miliyan 7.7 ga wani kamfani mai alaka da wani babban alkalin wasa.

Barcelona na fuskantar bincike daga hukumar kwallon kafar nahiyar turai UEFA, saboda zargin biyan wani kamfani miliyoyin daloli, wanda ke da alaka da wani alkalin wasa na kasar Sifaniya.

Hukumar ta UEFA ta ce a gudanar da bincike ba tare da bata lokaci ba kuma tuni masu shigar da kara sun dukufa domin gano gaskiyar lamarin.

Daga cikin ka’idojin gasar zakarun nahiyar turai, an haramtawa kowace kungiya wajen shirya sakamakon wasa ko wata badakala makamanciyar hakan.

Wasu takardun kotu sun nuna cewa Barcelona ta biya dala miliyan 7.7 ga wani kamfani mai alaka da wani babban alkalin wasa.