An tashi a wasan na semi-final ne da ci 1-1, wanda aka buga a Estadio Alfredo Di Stefano.
Dan wasan Chelsea Pulisic ne ya fara zura kwallo a minti na 14, sai Karim Benzama ya farke kwallon a minti na 29.
Duk da cewa Chelsea ta fi taka kwallo a wasan, musamman kafin a je hutun rabin lokaci, wasan wanda aka kare shi a cikin ruwa sharkaf, bai ba ta damar tafiya gida da makinta uku ba.
Kalubalen da ke gaban Madrid shi ne, sai ta lashe wasan zagaye na biyu da za a yi a Stamford Bridge a London nan da kwana bakwai.
Ita kuwa Chelsea, ta fara jin kamshin karawa da Manchester City ko Paris Saint Germain a wasan karshe da za a yi a ranar 27 ga watan Mayun 2021 a birnin Santanbul na kasar Turkiyya.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, kusan babu wani abu da ya sauya a wasan, yayin da duka bangarorin biyu suka yi ta kokarin kare kansu daga shammatar abokin hamayya.