Twitter Zai Sa Idon Mujiya Kan Sakonnin Shuwagabanni

Kamfanin Twitter zai fara sa ido kan rubuce-rubucen da shugabanni a fadin duniya keyi da suka karya dokokinsu, musamman bayanai da su kayi dai-dai da “ra’ayoyin jama’a,” kamfanin ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da wallafa a shafinsa jiya Alhamis.

Sai dai wannan mataki zai mai da hankali ne kawai a shafukan jami’an gwamnatin da aka tantance, da kuma 'yan takarkarun siyasa da suke da mabiya fiye da mutane dubu 100,000.

Amma dokokin kamfanin sun haramta duk wani nau’in labarai da ka iya janyo tashin hankali da yada ta’addanci, ko ci zarafin wasu.

Shi dai kamfanin a baya, yana barin duk wasu sakonnin da shugabannin duniya suka wallafa a kafar ko da kuwa ya karya dokokin su.

Kamfanin yace abinda suka fi maida hanakali akai shine, su kare yadda jama’a suke tattaunawa a shafukansu na Twitter, kuma wani abu mafi muhimmanci shine tabbatar da dokoki da kuma yadda muke aiwatar da su suna da saukin ganewa, a cewar sakon da kamfanin ya wallafa a shafinsa.