Turkiyya Ta Yi Gargadin Kar A Sabawa Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Syria

'Yan Gudun Hijirar Syria

Kasar Turkiyya ta yi gargadin cewa sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriya ka iya shafar tattaunawar zaman lafiyar da aka shirya yi wani lokaci a wannan watan.

Rasha da Turkiyya, wadanda ke goyon bayan bangarori daban-daban a wannan tashin hankalin, sun taimakwa wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta fadin kasar a makon jiya, wanda wata shimfida ce ta kokarinsu na tattaunawar zaman lafiya da za a yi a Astana, kasar Kazakhastan.

"Muddun mu ka kasa tsai da ci gaba da saba yarjajjeniyar da ake ta yi, to shirin tattaunawar zaman lafiya a Astana din ba zai yi nasra ba," a cewar Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu a hirarsa da kafar labaran gwamnati ta Anadolu a yau dinnan Laraba.

Dama manyan kungiyoyin 'yan tawayen Siriya sun yi nuni da saba ma yarjajjeniyar da gwamnati ta yi a matsayin dalilinsu na janyewa daga tattaunwar zaman lafiyar.