Turkiyya Ta Siya Makaman Kariya, Kirar S-400 Daga Rasha

Ma’aikatar tsaron kasar Turkiyya ta tabattar da cewa kasar a yau Juma’a, ta karbi rukunin farko na makaman kariya masu linzami kirar S-400 daga Rasha.

Karbar wannan makaman bangare ne na yarjejeniyar makaman da Turkiyya ta kulla tare da Rasha, kuma itace irinta ta farko da Rasha ta kulla da wata kasa daga cikin mambobin kungiyar NATO, abinda ke haifar da fargabar cewa Turkiyya tana kara kusantar Rasha.

Amurka ta yi kira da kakkausar murya da Turkiyya ta janye daga yajejeniyar da aka ruwaito ta kulla ta biliyyoyin dalar Amurka, inda har Amurka ta ke wa Turkiyya barazanar yiwuwar sakamata takunkumi ko kuma ta ki kera mata jiragen yaki da kamfanoninta suke yi na F-35.

Wanda hakan zai jawowa Turkiyya ta rasa biliyoyin dalolin Amurka na kwangilar da suka saka ma hannu.