Turkiyya Na Ba Da Guraban Karatu Kyauta Ga Matasa!

Muhammad Abdullahi

Kasar Turkiyya na samar da guraban karatu ga matasa masu sha'awar ci gaba da karatu a matakin gaba da Sakandare, wadnada suka fito daga ko'ina a duniya kuma kyauta.

Mohammed Abdullahi Garba, matashi dan asalin Jihar Borno, ya halarci makarantar firamari da sakandare a makarantar El-Kanemi College of Islamic Theology, daga nan ya samu shiga Jami'ar Maiduguri, sashen na “Physiotherapy” da kuma kiwon lafiya. Bayan kammala karatun digirin farko, ya nemi damar zuwa kasar waje don karo karatu.

Ya samu cin gajiyar gurbin karatu na kasar Turkiyya, inda ya tafi a matsayin dalibi da ya fara karatu daga farko a bangaren lafiyar dan’adam. A shekarar 2010 ya samu damar zuwa kasar Turkiya, inda ya halarci makarantar koyan yaren kasar.

Bayan kammala wannan karatun sai ya fara karatu a fannin likitancin iyali wato “Family Medicine” a turance.

Dalibai a fadin duniya na iya cin gajiyar guraben karo karatun na gwamnatin kasar Turkiyya, wannan wata dama ce da suke bama duk wani dalibi, da yake da karancin sakamakon jarabawar, kammala makarantar sakandare mai nagarta.

Kana duk wanda yake da sha’awar shiga cikin tsarin gurbin karatun, zai iya shiga idan har bai wuce shekaru 20 ba, babban abu da matasa za su bukata, shi ne su ziyarci shafin www.turkiyeburslari.gov.tr wanda za su samu damar cika fom don samun garabasar guraben karatu a matakin digirin farko.

Gwamnatin kasar ba ta tsaya kawai ga karatun digirin farko ba, har ma da matasa masu sha'awar karatu a matakin digiri na biyu, da na uku wato digirin digirgir.

Duk ana iya samun wannan damar idan matasa na da sha'awar karo karatu, kuma ba su da zarafin yin hakan.