Turkiya Ta Kai Hari Kan Kurdawa Dake Cikin Iraq

Shugaban TurkiyyaRecep Tayyip Erdogan wajen fafutikar neman kuri'a a zaben da za'a yi wannan watan

A kokarin farfado da martabarsa tare da neman sake cin zabe, shugaban Turkiya Recep Tayip Erdowan ya sanar da kai harin soja ta sama akan kurdawa 'yan aware dake cikin Iraq

Shugaban kasar Turkiyyar Recep Tayip Erdowan ya bada sanarwar harin sojan da aka kai wa kurdawa ‘yan aware a babban tungansu dake Iraqi. Erdowan ya dauki wannan mataki ne a yayinda ya auna begen samun kuri’ar yan kishin kasa musammam akan zaben da za a yi a wannan watan.

Tun ranar Littini ne dai aka bada labarin luguden wuta da jiragen saman yakin Turkiyya keta yiwa yankin Qandil,sai dai ba wani labarin cewa ankai hari ta kasa.

Nasarar wannan harin zai kara wa Erdowan kwarin gwUiwar fara fafitikar yakin neman zaben sa dake tangal tangal.

Kuriar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa Erdowan yana samun komawa baya, farin jininsa kuma ya na raguwa. Ga bisa dukkan alamu koda zai yi nasara to ba dai kai tsaye ba sai an tafi zagaye na biyu.