Turkawa Sun Amince Da Sauye-Sauye Ga Tsarin Mulki

Kashi 58 cikin 100 na masu jefa kuri'a suka yarda da wadannan sauye-sauye ga tsarin mulkin da sojoji suka rubuta shekaru 30 da suka shige

Firayim ministan Turkiyya yace kimanin kashi 58 cikin 100 na masu jefa kuri’a sun amince da sauye-sauye ga tsarin mulkin kasar wanda aka rubuta shekaru 30 da suka shige karkashin mulkin soja. Firayim minista Recep Tayyip Erdogan shi ya bayyana wannan jiya lahadi, jim kadan a bayan da aka jefa kuri’a kan sauye-sauyen.

Yace kimanin kashi 77 zuwa kashi 78 cikin 100 na masu jefa kuri’a suka fito suka kada kuri’unsu. Turkawa miliyan 49 ne suka yi rajistar shiga zaben na jiya lahadi, wanda aka yi a ranar cikar shekaru 30 da juyin mulkin da sojoji suka yi a 1980.

Masu jefa kuri’ar su na da zabi biyu ne kawai, yarda ko kuma kin yarda da wadannan sauye-sauye guda 26 wadanda gwamnati ta ce zasu gusar da kasar ga tsari irin na Turai. Ana daukar wadannan sauye-sauye a zaman masu muhimmanci a kokarin Turkiyya na shiga Tarayyar Turai.

Tashin hankali ya kawo cikas ga kuri’ar a birane da dama. ‘Yan sanda a fadin kasar sun tsare mutane 138 saboda kuntatawa masu jefa kuri’a ko kuma dai neman da su tilasta musu goyon bayan wani bangare.

Jiya lahadi, shugaba Barack Obama na Amurka ya buga ma Mr. Erdogan waya, inda ya fada masa cewa yawan mutanen da suka fito jefa kuri’a ya nuna irin karfi da kwarjinin dimokuradiyya a Turkiyya.