Kwararru a fannin adana ruwa sun shawarci manoma a Afirka da Asiya da su samo sabbin dabaru na adana ruwa a zaman wani mataki na rigakafin karancin ruwan sama da ake samu a saboda sauyin yanayi.
Wani sabon rahoton da Cibiyar Kula da Ruwa ta Duniya mai hedkwata a kasar Sri Lanka ta bayar yace mutane kusan miliyan 500 zasu amfana daga kyautata kula da ruwa ko adana shi.
Rahoton ya bayar da shawarar da a kaucewa dogaro kan manyan ayuuka, kamar gina manyan madatsu, domin adana ruwa, a gwada wasu dabarun. Sabbin dabarun da cibiyar ta bayar da shawarar dauka sun hada da janyo ruwa daga fadamu, ko kuma daga rijiyoyi a kasa, tare da tara ruwa a cikin gulbi, ko tanki da kananan ramuka.
Kwararrun suka ce idan ruwa ya ja a daya daga cikin wadannan, to ana iya komawa ga wata daga cikinsu.
Rahoton ya ce an samu nasarar gwajin samar da kananan wuraren adana ruwa a kasashen Nijar da Zimbabwe da Indiya da kuma China.