Tunisa: Dakarun kasar sun hallaka mayakan sa kai 21

Firayim Ministan Tunisia Habib Essid yana jawabi akan harin da 'yan ta'ada suka fara kaiwa kafin dubunsu ya cika yau Litinin

Kasar Tunisia ta sha fama da samun hari daga 'yan ta'ada dake neman tilastawa kasar kakatawa ga tasu irinakidar

A yau Litinin Ministan cikin gidan Tunisia ya fada cewa dakarun kasar sun kashe mayakan sa kai 21, wadanda suka kai hari a wani ofishin ‘yan sanda da wani sansanin sojin kasar da ke kusa da kan iyakar kasar Libya.

Jami’an sun ce an kashe akalla fararen hula hudu da wani soja guda a arangamar da aka yi a garin Ben Guerdane dake kudu maso gabashin kasar.

Bayan arangamar, hukumomi sun umurci mazauna yankin da su zauna a cikin gidajensu.

Dakarun kasashen yammacin duniya dai na taimakawa takwaroinsu na Tunisia, yayin da ake kara nuna damuwa, kan yadda mayakan sa-kai, ciki har da na kungiyar IS ke tsallaka kan iyaka domin kai hare-hare.

A makon da ya gabata, Burtaniya ta bayyana cewa za ta aika da dakarunta 20 da za su taimaka wajen kare kan iyakar.