Ma’aikatar harkokin wajen kasar Italiya ta shaida cewa a jiya laraba ne aka gano gawar matashin mai suna Giulio Regeni a wata unguwa da ke bayangarin Al-kahira, a kan hanyar da ke zuwa birnin al-Askandariya. An same shi da kuna da wasu raunuka a jikinsa, abin da ke nuna cewa ta yiwu an azbtar da shi kafin mutuwarsa.
Ma’aikatar ta harkokin waje ta kira jakadan Massar da ke Rome akan hukumomin Masar su bada cikakken goyon baya a binciken da za a yi game da mutuwar Regeni, ciki har da sanya hannun kwararrun Italiya.
Regeni dai dan shekaru 28 da haihuwa a duniya ne, ya yi karatu a jami’ar Cambridge da ke britaniya, da ga nan ya je Masar don neman bayanan wani kwas da ya ke yi na babban digirin PhD. Hukumomin sun fadi cewa Regeni ya je ganin abokinsa ne a cikin garin na Al-kahira a lokacin da ya bata ranar 25 ga watan da ya shige, ranar da aka cika shekara 5 da hambare gwamnatin shugaba Hosni Mubarak.