WASHINGTON DC —
Biyo bayan jerin dimbin takunkuman da ECOWAS ta kakaba wa jamhuriyar NIJAR bayan da sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasa su ka hambarar da zababbiyar gwamnatin farar Hula ta BAZOUM MOHAMMED, wannan ya ja hankalin masana.
A wannan kashi na karshe na tattaunawa da DR. Umar Ardo da ke zama kwararre kan sha'anin tsaro kuma tsohon malami a makarantar horas da hafsoshin sojojin Najeriya wato NDA, ya yi karin haske kan yadda aka matsa wa sojojin da su ka yi juyin mulkin.
Saurari shirin:
Your browser doesn’t support HTML5