TUBALIN TSARO: Ganawar Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar Sojin Najeriya Da ‘Yan Jarida, Fabrairu 23, 2024

HAssan Maina Kaina

Jagoran sojojin Najeriyar ya magantu kan irin kokarin da suke yi na yaki da ta'addanci a cikin kasar, batun binciken harin da soji suka kai kan masu Maulidi a Tudun Biri, kalubalen da sojojin ke fuskanta na karancin makamai da kuma ko gaskiya ne Faransa ta girke sojojinta bataliya biyu a Najeriyar.

Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar Tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ya gana da wasu zababbun 'yan jarida da ke aikewa da rahotanni kafafen watsa labarai na kasashen waje inda ya tabo batutuwa daban-daban dangane da sha'anin tsaro.

Saurari cikakken shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

TUBALIN TSARO: Ganawar Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar Sojin Najeriya Da ‘Yan Jarida.mp3