Ga dukan alamu Majalisar Dokokin jahar Adamawa ta samu biyan bukatar ta, ta neman a kafa kwamitin da zai gudanar da binciken tabbatar da hujjojin tsige gwamnan jahar Murtala Nyako da Mataimakin shi Barrister Bala James Ngillari.
Bayan bukatar da majalisar ta gabatar a kwanakin baya, mukaddashin Cif Jojin jahar ta Adamawa Ambrose Mammadi ya kafa kwamitin mutane bakwai wanda zai gudanar da bincike a kan gwamnan jahar da mataimakin shi.
Your browser doesn’t support HTML5
Babban rajistara na babbar kotun jahar Adamawa, Abubakar M.Bayola ne ya sanya hannu a kan takardar sanarwar kafa kwamitin.
Mukaddashin Cif Jojin Ambrose Mammadi ya kafa wannan kwamiti ne a daidai lokacin da gwamna Murtala Nyako ke wanke gwamnatin tarayya daga zargin cewa ita ce ta kitsa kulle-kulle ta da kumbiya-kumbiyar tsige shi daga mukamin shi na gwamna.
Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Jahohin Adamawa da Taraba, Ibrahim Abdulaziz ne ya aiko da rahoton.