Tsohuwar Kwamishanar Jihar Borno ta Tsallake Rijiya da Baya

Civilian JTF

Cikin 'yan kwanakin nan a jihar Borno, musammana wajejen dake makwaftaka da babban birnin Maiduguri sun shiga wani halin lahaulawalakawati inda ake ta samun asarar rayuka.

Tsohuwar kwamishana ta ma'aikatar yaki da talauci ta jihar Hajiya Ya Gana Muazau ta tsallake rijiya da baya a hannun wasu matasa da suka hallaka masu gadinta guda biyu kana suka bankawa motar da take ciki wuta har ta kone kurmus a lokacin da suke kokarin tsira da rayukansu. Lamarin ya faru ne sanadiyar harin da aka kai kan barikin Giwa a birnin Maiduguri.

Wanan harin har ya sa mutane da dama sun fice daga gidajensu. Maharan da suka kutsa cikin barkin sun samu sun saki 'yanuwansu dake tsare yayin da kuma mutanen gari musamman matasan da ake kira "Civilian JTF" suka bi maharan suna kamasu suna kuma mikasu ga hukumomin tsaro. Wanda kuma ya gamu da ajalinsa nan take za'a hallakashi.

Bayan harin, yadda matasan suka dinga farautar mutanen da suke zargi da yin ta'adanci da yawan barin wuta tsakanin sojoji da 'yan ta'adan sun janyo korafe-korafe cikin jama'a. Dalili ke nan da duk wadanda suke da gidaje kewaye da barikin suka soma kauracewa gidajensu.

Ita ma tsohuwar kwamishanar da gidanta na kusa da barikin sai ta kwashe nata-i-nata domin ta kaurace daga anguwar. To saidai yayin da take gudu daga anguwarta sai ta fada hannun wasu. A gaban idanunta aka danddatse daya daga cikin masu gadinta har lahira kana aka kone guda da wuta kafin a bankawa motar da take ciki wuta. An yi kokarin hallakata to amma Allah Ya kiyayeta

To saidai Barrister Jibrin Gunda mai baiwa "Civilian JTF" shawara yace ba 'yan kungiyar ba ne suka aikata domin suna yin aikinsu bisa ga kaida da doka da oda. Yace ya cigaba da sasu a hanya yadda ya kamata. Irin wadannan korafe-korafen a ke samu domin har yanzu mutane na bacewa nan da cana a birnin na Maiduguri.

Ga karin bayani