Tsohuwar Jakadiyar Amurka A Ukraine Tace Trump Ne Ya Matsa A Dakatar Da Ita

Tsohuwar jakadiyar Amurka a Ukraine Marie Yovanovitch ta fadawa kwamitocin majalisar wakilan Amurka dake jagorar binciken yiwuwar tsige shugaba Donald Trump cewa shugaba Trump ya hurawa ma’aikatar harkokin wajen kasar wuta akan su cire ta daga mukamin jakadiya.

Jaridar Washington Post ce ta fara bayyana wannan rahoton, wanda ta ce ta samo daga jawabin da Marie ta shirya gabatarwa a gaban kwamitocin.

Trump ya dakatar da Marie daga zama jakadiyar Amurka a Ukraine a watan Mayun da ya gabata bayan ikirarin wasu bayanai marasa tushe dake cewa ta nemi ta rushe manufofin shugaban.

A bayanin jawabin da ta shirya, tsohuwar jakadiyar ta fadi cewa matakin da shugabannin ta suka dauka na cire ta daga mukamin sun yi ne bisa bayanai marasa tushe na karya kuma daga mutanen da akwai alamar tambaya a dalilansu.

Tsohuwar jakadiyar ta ce ta yi mamakin cire ta daga wannan mukamin da aka yi duk da cewa ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yarda cewa ba ta aikata wani laifi ba.