Tsohuwar ministar dai tun makon da ya gabata ne ya kamata ta bayyana a ofishin na EFCC, amma dai bisa rahoton da jaridun cikin gida na Najeriya sun bayyana cewa tsohuwar ministar bata sami zuwa ba.
Abuja, Najeriya —
Tsohuwar Ministar Ayyukan Jin Kai ta Nijeriya Sadiya Umar Farouq ta gabatar da kanta a gaban hukumar EFCC a Abuja babban birnin Nijeriya.
Tsohuwar ministar dai tun makon da ya gabata ne ya kamata ta bayyana a ofishin na EFCC, amma dai bisa rahoton da jaridun cikin gida na Najeriyan suka bayyana, tsohuwar ministar bata sami zuwa ba.
Ana zargin wani dan kwangila na ma’aikatar a zamanin ministar da almundahanar makudan kudade sama da naira biliyan 37.
A safiyar Litinin din nan ne tsohuwar ministar ta wallafa a shafinta na X inda ta sanar da bayyanar ta ga ofishin hukumar ta EFCC.