Tsohon Shugaban Panama Manuel Noriega Ya Rasu

Tshon shugaban mulkin kama karya a Panama Manuel Noriega, wanda tarzoma da cin hanci da rashawa suka mamaye mulkinsa, ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.

Shugaban kasar Juan Carlos Varela, ya fada ta shafin Twitter cewa, mutuwar Noriega "ta rufe wani babi a tarihin kasar, kuma akwai bukatar a baiwa iyalansa damar yin jana'izarsa cikin lumana.

Noriega ya kwanta a asibiti, inda yake murmurewa daga tiyatar da aka yi masa na cire masa sankara a kwakwalwarsa.