Tsohon Shugaban Nijar Tanja Mamadou Yana nan Da Ransa

Tsohon shugaban Nijar Tanja Mamadou

A jamhuriyar Nijer makusantan tsohon shugabann kasa Tanja Mamadou sun karyatar da labaran da aka yi ta yadawa a yau Asabar a shafin facebook cewa ya rasu.

Wannan shine karo na biyu da ake bada labarin rasuwar Tanja Mamadou a kasar ta Nijer, amma kuma daga bisani ake cewa babu kanshin gaskiya.

labarin rasuwar shugaba Tanja Mamadou wanda ya bayyana da hantsin wannan rana ta Asabar 14 ga watan Disamba ya matukar daukar hankalin jama’a a bisa la’akari da yadda abin ya mamaye kafafen sada zumunta yayin da mutane daga ciki da wajen kasar ta Nijer suka yi ta bugawa juna waya domin jin gaskiyar lamari.

Wani na hannun damar Tanja, wato Alhaji Nouhou Arzika ya karyatar da wannan labari.

Faruwar wannan al’amari ya sa wasu ‘yan kasa jan hankulan jama’a a game da mahimancin amfani da kafafen sada zumunta ta hanya mafi a’ala a maimakon amfani da irin wannan kafa don tayar da zaune tsaye.

Tanja Mamadou wanda ya shugabanci kasar Nijer a zamanin jamhuriyar ta biyar ya yi nasarar sauya al’amura a game da yadda ake gudanar da harakokin ma’adanan karksahin kasa, inda ya tilastawa shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy a shekarar 2008 zuwa Nijer domin su tattauna akan huldar cinkiyyar karafun nan uranium din da Faransa ta shafe shekaru kusan 40 tana hakowa a yankin Agadez, amma kuma al’umar Nijer ba ta morar wannan arziki.