NIGER, NIGERIA - To amma Dakta Jonathan ya ce ya zo Minna ne domin gaisuwa ga wadannan tsoffin shugabanni, amma dai ya yi amfani da wannan dama wajan yin kira ga ‘yan Nigeria da su zabi shugaban da Najeriya ce a gabansa.
Ya kuma kara da cewa “dukkaninmu muna yi ma kasarmu fatan alheri ga matasanmu kuma zabe na zuwa ya zama wajibi mu zabi wanda zai mana shugabanci na gari, mutumin da Najeriya ce a gabansa ba wai biyan bukatunsa ba”
Tuni dai masu sharhin siyasa suka fara fashin baki akan wadannan kalamai na tsohon shugaba Jonathan, wanda babban jigo a babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Nigeria, Kabiru Abubakar Mai Jama’a na daya daga cikin masu sharhin ya ce "maganar Jonathan abin dubawace."
Yanzu haka dai gidajen wadannan tsoffin shugabannin da ke saman tsaunin birnin Minna na ci gaba da samun bakin manyan ‘yan siyasa, al’amarin da masu sharhin ke alakantawa da babban zaben kasar na shekarar badi.
Saurari rahoto Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5