Buhari Ya Yaba Wa APC Kan Sakamakon Zaben Imo Da Kogi

Shugaba Buhari (Facebook/Femi Adesina)

Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba, ya taya jam’iyyar APC murnar lashe zaben gwamna a jihohin Imo da Kogi.

A cikin wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawunsa ya rabawa manema labarai, Buhari ya godewa al’ummar jihohin biyu "saboda sake jaddada amincewarsu da babbar jam’iyyar siyasar kasar.

Tsohon shugaban ya bayyana godiyarsa musamman ga shugabannin jam’iyyar APC da ma'aikata, wadanda ya ce sun yi namijin kokari wajen ganin samun nasarar Hope Uzodimma a karo na biyu a jihar Imo, da kuma Ahmed Usman Ododo a matsayin gwamnan jihar Kogi mai jiran gado.

An dai gudanar da zaben gwamnoni a jihohin ne a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamban 2023.