Tsohon Shugaban Isra'ila Shimon Peres Ya Rasu

APTOPIX Mideast Israel Obit Ariel Sharon Shimon Peres Israel

Tsohon shugaban Isra’ila kuma tsohon frayim-ministanta Shimon Peres, wanda ake cewa ya share tsawon duk shekarun kafa Isra’ila yana bauta mata, ya rasu, yana da shekaru 93 a duniya.

Peres, wanda ya fuskanci kasawar jikinsa kamar makkoni biyu da suka wuce, ya rasu ne yau Laraba a wata assibiti dake HaShomer.

Kusan duk wani babban mukmamin siyasa da ake rikawa a kasar tashi – ka ma daga Frayim minister, ministan tsaro, ministan harakokin waje da shugaban kasa – duk Peres ya rika su.

Haka kuma a duk tarihin Isra’ila shine yafi kowa dadewa yana zaman Dan-majalisar Dokokin kasar, mukamin da ya rike na tsawon shekaru 48.

Kuma, abin mamaki, Peres ba ma dan kasar Isra’ila na asali bane, a kasar Belarus aka haife shi, ya koma Isra’ila ne da zama yana yaro dan shekaru 11 kacal da haihuwa, lokacin ma Isra’ila na karkashin mulkin mallakar Birtaniya.