Tsohon Shugaban Chadi Hissene Hare Ya Gurfana Gaban Kotu a Senegal

Hissène Habré tsohon shugaban Chadi da ake zarginsa da yiwa dubban mutane kisan gilla

Wata kotu ta musamman a Senegal, ta fara sauraren karar tsohon shugaban kasar Chadi, Hissene Habre, wanda ake tuhuma da aikata laifukan yaki da suka shafi cin zarafin bil adama.

A baya, Mr. Habre, ,mai shekaru 72 da kuma lauyansa, sun yi watsi da tuhumar kotun, suna masu cewa kotun ba ta bin ka’ida, saboda haka ba za su shiga cikin karar ba.

Amma a yau Litinin, Habre ya halaraci zaman kotun, bayan da hukumomi suka tilasta masa gurfana a gaban kotun.

An dai kafa kotun ne bisa wata yarjejeniyar da kasashen Tarayyar Afrika suka kulla, za kuma ta saurari bahasi daga shaidu 100 a wannan shari’a da ake sa ran za a kwashe watannin da dama ana yi.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da wata kungiyar tabbatar da adalci a kasar Chadi, suna zargin Habre da laifin hanu a kisan da akawa fiye da mutane dubu 40 da ake dangantawa da siyasa, da azabtarwa a lokacin da ya ke mulki. Habre ya shugabanci Chadi a shekarun 1982 da 1990, inda daga baya shugaba mai ci na yanzu Idriss Deby ya hambarar da gwamnatinsa.